Friday, 5 September 2014

Yen Arewa A Yau, Shin Wai Ina Mafita? ~ Usama Dandare

Masu iya salon magana kance: "da akwai hannun biri a cikin miya, idan ba a cire ba, za a yi tsammanin cewa hannun mutum ne."

Ina ganin basai Mahadi ya bayyana ba kamin ka yarda cewa Boko Haram wani shiri ne kawai da wasu makiyan Arewa suka kirkira domin su cimma wata manufa, wata kila manufar siyasa ko kuma wata manufa can da sukadai suka san da ita. Amma babu tambaba, kungiyar Boko Haram an kirkiro ta ne domin a rage yawan mutanen arewacin Nigeria, a kuma gurgunta dukiyoyin su.

Idon kayi la'akari da irin tsarin hareharen da yen Boko Haram ke kaiwa a arewacin kasar nan da kuma yadda gwamnati keyin halin koh oho da kisan gillar da yen ta'adda ke yiwa yen arewa da mazauna cikinta, dole kayi zargin cewa akwai hannun wasu daga cikin jami'o'in gwamnati a cikin ta'addancin Boko Haram, don ko bazai yiwu gwamnati ta saka ido tana kallon yadda ake kashe yen kasarta ba in har babu wani ra'ayi a ciki.

Zan iya in amince in kace mani ba shugaba Jonathan ya kirkiro Boko Haram ba kuma bashi ke sa suna kashe mutanen arewa ba, amma bazan yarda ba in kace ba wata ribar da Jonathan ke samu a dalilin ta'addanci Boko Haram, ko ribar siyasa ko kuma ribar dukiya. In ba haka ba, miye makasudin da gwamnatin Jonathan taki bada himma wajen kawarda Boko Haram da ta'addanci a Arewa?

Akwai misalai da yawa da suka faru a kasar nan wadanda dole zasu saka mutum yin zargin gwamnati da hannu cikin kashe-kashen da akeyi a arewacin kasar nan, da akwai lokaci mai yawa dana zayyano maku su gaba daya amma ga kadan daga cikinsu. Biyo ni kusha labari, lallai akwai hannu biri a cikin miya.

Lokacin da aka kama tsohon shugaban kungiyar Boko Haramun Mohammed Yusuf, shin ko kun taba tambayar dalilin da yasa yensanda suka kashe shi ba tare da an gurfanar dashi a gaban kuliya ba? An kashe shi ne domin a fusata yen kungiyar sa domin a hassasa wata rigima a Arewa da zata bata hurumin yiwa yen Arewa kisan gilla.

Bam din daya tashi na daya ga watan Octoba a Abuja wanda kungiyar ta'addanci ta MEND ta dauki alhakin tayar wa yazo da wani abun ban mamaki, yanda shugaba Jonathan ya zaburo ya karyata kungiyar MEND da cewa basu suka tayar da bam din ba, shi yasan wadanda suka tayar dashi tun kamin hukumomin tsaro su fara bincike akai, wai wasu yen siyasar Arewa ne da basu son sa a kan mulki. Wannan shiya nuna Jonathan nada wata azazza da bakar anniya tsakanin sa da arewacin Nigeria.    

Bayan yen kungiyar Boko Haramun sun zaburo da kai harere da kuma kisan mutane ba tare da wani dalili ba, jigajigan Arewa sun tayar wa shugaba Jonathan kayar baya cewa dole ya yiwa yen kungiyar afuwa (amnesty) kuma a zauna dasu ayi maslaha domin cimma zaman lafiya a kasa baki daya, Jonathan ya bada umurnin cewa su zo ayi sulhu amma ba acikin son ransaba. Jim kadan bayan sanarwa, Jonathan da kungiyar kiristoci ta CAN suka shaida wa duniya cewa yen Boko Haram ba zasu aminta da wannan sulhun ba, kuma hakan ya faru basu aminci ba. Shin a ina Jonathan da CAN suka samun shaidar cewa Boko Haram ba zasu aminta da amnesty ba? Labarin cikin gida sai dan cikin gida.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamurran tsaro, wato Gen Azazi da yake bai iya satar matan makwabta ba, ya fito fili ya bayyana cewa akwai yen Boko Haram a cikin gwamnati tare kuma da shugaba Jonathan, dalilin daya sa aka kashe shi a cikin jirgin sama don ya tona asirin manyan gwamnati kuma ansan in aka gyele shi, zai ci gaba da tonon asiri.

Wata majiya mar tushe ta shaida cewa kauyukan dake kusa ga dajin da yen Boko Haram suke, suna ganin saukar jiragen sama (helicopters) suna saukar wa da yen ta'addan abinci da kayan yaki. So kake ka gayamun cewa jirgi zai iya tashi har yayi yawo a sararin samaniya ba tare da masaniyar gwamnati ba? Bayan akwai hukumomin dake da hakkin kula da tsaron sararin samaniya.

Ka taba zaunawa kayi tunanin ina Boko Haram ke samun kuddin shiga da kuma makaman yaki? Gwamnati ce ke baiwa yen Boko Haram makamai ta hanyar sojojin Nigeria, za'a tura sojoji sukai makamai zuwa wani guri amma sai kaga Boko Haram sun zo kan hanya sun kwace makaman gaba ba tare da anyi wani barin wuta ba tsakanin su da sojoji. Ko kuma gwamnati ta ajiye makamai a barinkin soji ko yensanda, bayan jim kadan sai kaga yen Boko Haram sun zo sun hargitsa wurin sun tafi da makaman gaba daya.

Ya faru sau yafi a kirga in da yen Boko Haram zasu kawo hari amma sai a tarar da sojojin dake gurin sun yi sama ko kasa, sai can bayan yen ta'addan sun kammala ta'addancin su sai kaga sojojin sun dawo suni halbin mutanen gari da basu san hawa ba balle sauka, amma har yau gwamnati ta kasa ansa tambayan nan: waye yake baiwa sojoji damar da su bar gurin da suke tsaro kamin zowar yen Boko Haram? A wane dalili sojoji zasu gudu subar wurin aikinsu ba tare da amince war shuwagabannin su ba? Hmmm!! Akwai hannu biri a cikin miya.

Sakarci da sakakancin mulkin Jonathan bangaren samarwa sojoji kayan aiki masu inganci ya sanya sojojin kasar nan cikin wani halin ha'ulla'i har ankai lokacin da sojoji suke aron ta kare idan sunji ance ga yen Boko Haram nan zuwa, kwanakin nan wurin soja dari biyar suka haura zuwa kasar Cameroon don neman mafuka daga harin yen Boko Haram. Abun ban mamaki shi ne yadda Goodluck Jonathan keyin kasafin makudan kudi bangaren harakar tsaro amma har yau, sojojin mu nacan ana famar kashin su sanadiyars rashin kayan aiki na kwarai.

Abin tambaya anan shine; ina gwamnati ke kai makudan kuddin da ake ware wa sashen tsaro a Nigeria? Ina makaman da gwamnati ke karyar cewa an sayo wa sojojin Nigeria? Shin gwamnati ta taba binciken wadanda ke da hannu cikin sayen makamai a kasar nan? Lallai akwai alamar tambaya.

Rahotanni daga hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa gwamnati bata basu isassun makaman da zasu tunkari yen kungiyar Boko Haram, amma kullun muna jin labarai na karya daga gwamnati dake nuni ga nasara kan fada da ta'addanci da akeyi a Nigeria kuma wani abin ban mamaki shine yadda yen ta'addan ke cigaba da samun galaba akan sojoji, har sun kai ga kwace garuruwa da dama daga hannu gwamnati.

Shin wai ina dubban yen Boko Haram da hukumomin gwamnati ke cewa sun kama tun shekara biyar da suka wuce zuwa yau. Ana nufin har ilawa yau ma'aikatan tsaro sun kasa samun bayanan shirri daga yen Boko Haram din da ake tsare dasu, bayanai masu fa'ida da za'ayi amfani dasu gurin kama sauran yen ta'addan dake da hannu cikin tashetashen hankula a kasar nan?

Na tabbatar da Jonathan bazai tsaya yana iskanci ba inda yen Boko Haram a Bayelsa suke yin ta'addancin su amma yanzu ba ruwansa tunda a Arewa sukeyi, ba abunda ya shamar kar tunda yen Arewa ake kashewa ba mutanen garinsu ba.

Wani abun haushi shine yadda gwamnati Jonathan take nuna ra'ayin sha'awa ga yaduwar ta'addanci ke yaduwa a Arewa. In kun tuna, wani bature mai sulhu tsakanin gwamnati da yen Boko Haram ya bayyana cewa Senator Ali Modu Shariff da Gen Ihejirike ne manya manyan shuwagabannin Boko Haram amma har ilawa yau, gwamnatin Jonathan tayi kunnen kurma akan maganar kuma taki hukunta Ali Shariff da Ihejirike, kin yin haka ya nuna cewa gwamnatin Jonathan batason ta kai karshen Boko Haram.

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako ya kalubalanci gwamnati da cewa tana da hannu a cikin tashe tashen hankula dake faruwa a Arewa, ya kuma nuna baccin ransa akan yanda gwamnati ke wasa da kisan gilla da ake yiwa yen arewacin kasar nan, dalilin kenan dayasa shugaba Jonathan yayi makasudin tsige Nyako daga kujerar gwamna domin yana neman tona masa asiri.      

Ina ganin duk wata manufa da ake son a cimma bangaren tarwatsa Arewa an cimmata, koma su waye suka kirkiro boko Haram toh sun cimma bakin nufinsu don yen arewacin Nigeria a yau mun shiga wani matsanaicin hali na ha'ula'i, dukiyoyin Arewa sun tarwatse kuma mutanen dake cikinta sun zama abin banza da rayuwar su ba bakin komai bace.

Muna cikin wani yanayi na bakin ciki da bacin rai, mun shiga wani yanayin bala'i da azaba da masifa da kunci da kuma wulakanci, rayuwar dan Arewa a yau ba bakin komai bace, ankashe maza, ankashi kananan yara, an kama mata, an kona makarantu, an kona asibitoci, a kona masana'antu an kuma tarwatsa rayukan mu amma duk da hakan, wasu makiyan Arewa na cigaba da yada maganganun banza wai yen Arewa ne ke kashe kansu don basu son mulkin Jonathan.

Babban abin bakinciki a yau shine bayan duk halin kunci da muke ciki a Arewa, da kuma yadda gwamnati Jonathan tayi ko oho da irin yanda ake yiwa yen Arewa kashin gilla, wasu tsirarru marasa kishin Arewa sun sha alwashin taimakawa da tabbacin yiwa Jonathan hidimar da zata sa ya samu galabar komawa kan mulki karo na biyu.
Wannan babban abin bakin ciki ne, domin kuwa ba dalilin da zai sa wani ko wata mai kishin Arewa yayi mubaya'a ga gwamnati Jonathan bayan itace gwamnati da bata damu da kisan yen Arewa ba, sannan itace gwamnati wadda kecin riba a kashekashen da akeyi a arewacin kasarnan. Shin miye hujjojin su da suke son Jonathan ya koma kan mulki bayan bai kullawa Arewa komai ba bayan haddasa bala'i da masifa a Arewa? Son suke Jonathan ya koma kan mulki don acigaba da kisan yen Arewa koh tsabar rashin kishin Arewa ne, ko kuma suna da hannu a cikin tashin hankulan dake faruwa a yau? Kaicho, bahaushe mai ban haushi.

Yen Arewa ku farga, ku farka daga bacci, ku tashi ku kare kanku da dukiyoyin, ku fito ku kori makiyanku dake amfani da rayuwarku don cimma wata banzar manufar siyasa koh neman arziki. Ku daina dogara kan wadannan manyan Arewa marasa amfani dake cikin gwamnati, bazasu iya canja matsakaicin halin da muke ciki ba yanzu, manyan banza ne marasa kishin Arewa dake amfana da rabe raben kawuna da gwamnati Jonathan ta kirkira da kuma zubar da jinin yen Arewa da akeyi.

Yen Arewa, shin wai ina mafita? Zaku zauna ne kuna kallon gwamnati Jonathan tana wasa da rayukan ku, ko zaku yiwa kanku kiyamul laili kuyi waje da Jonathan da mukarraban sa ranar zabe? Shin zaku saka ido ku kyele Jonathan ya koma kan mulki acigaba da kisan ku daya bayan daya? Zaku amince da wasu yen Arewa marasa kishi dake neman Jonathan ya koma kan mulki? Zaku zabi shugaba na gari da zai kare maku darajjar ku da rayukan ku da kuma dukiyoyinku koh zaku bar Jonathan ya koma mulki har a kashe ku gabadaya?                

Ina fatar zaben 2015 zai zama zabe na farko da yen Nigeria musamman yen Arewa zasuyi tsaye su zabi mutun na gari kuma zasu jure duk wata barazana da gwamnati ke takamar yiwa Arewa a lokacin zabe.

No comments: